Official

Welcome to Nasiriyya

Nasiriyya is now ready as a digital movement platform.

Ɗan siyasa mai farar aniya ba sai ya yi ta tallata kansa da surutu ba; ayyukansa da kusancinsa da jama’a su ne suke yi masa magana.
Nasir Yahaya mutum ne da za ka same shi a cikin al’ummarsa a kowane lokaci; ba wai sai lokacin siyasa ba, ba wai sai lokacin neman ƙuri’a ba. Yana cikin jama’a kamar ɗaya daga cikinsu, yana sauraron damuwarsu, yana jin ƙorafinsu, yana kuma nuna cewa shugabanci ba kujera ba ce kawai, hidima ce.
Wannan kusanci, sauƙin kai, da son jama’a su ne suka bambanta shi da sauran ’yan siyasa. A lokacin da wasu ke nesa da talakawa, shi yana nan cikin su. A lokacin da wasu ke jira a neme su, shi yana neman hanyar da zai kasance tare da jama’arsa.
Saboda haka ne Nasir Yahaya ya zama gagara badau; jagora mai tasiri, ɗan siyasa mai farin jini, kuma mutum da al’umma ke ganin darajar shugabancinsa a aikace ba a baki kawai ba.
Allah ya ƙara masa basira, ƙarfi, da ikon ci gaba da yi wa al’umma hidima.